Commons:Wiki Loves Monuments/Binciken DEI 2022/Rahoton ƙarshe/Me ke cikin batutuwan

This page is a translated version of a page Commons:Wiki Loves Monuments/DEI research 2022/Final report/Pipeline and the translation is 100% complete. Changes to the translation template, respectively the source language can be submitted through Commons:Wiki Loves Monuments/DEI research 2022/Final report/Pipeline and have to be approved by a translation administrator.
Bayani Gabatarwa Abin koyo Shawarwari Matsalolin da za'a iya fuskanta Me ke cikin batutuwan? Ƙarin bayanai



Yanzu menene a gaba?

Tawagar WLM ta ƙasa da ƙasa tana tattaunawa da Wikimedia Sweden da Wiki Loves Africa don kafa cibiyar sadarwa na shirin farko ga cibiyoyin cikin gida da masu shirya WLM na ƙasashe a Afirka. Shirin na farko zai mayar da hankali ne kan ƙasashe biyar na Afirka waɗanda suka haɗa da (Kenya, Afirka ta Kudu, Ghana, Zimbabwe da Uganda) da nufin samar da wani wuri, ƙarfafa tattaunawa da kuma taimakawa al’ummar WLM wajen samun mafita da goyon baya wajen samar da gasa mai inganci.

Bayan shekaru biyu ba tare da ɗan ƙaramin haɗuwa ba saboda ɓarkewar annoba, ƙungiyar WLM- ta ƙasa da ƙasa za ta sake haɗuwa a zahiri kenan a karon farko bayan taruka ta intanet, WLM kuma tana da niyyar kawo wasu dabarun shekaru masu yawa nan da wasu shekaru masu zuwa. Sakamakon wannan binciken zai kasance ɗaya daga cikin batutuwan da za'a tattauna kuma a adana su don aiwatar da dabarun a nan gaba.

← Baya | Yi baya zuwa wurin jawabin rahoton →