Commons:Wiki Loves Monuments/Binciken DEI 2022/Rahoton ƙarshe/Gabatarwa

This page is a translated version of a page Commons:Wiki Loves Monuments/DEI research 2022/Final report/Introduction and the translation is 100% complete. Changes to the translation template, respectively the source language can be submitted through Commons:Wiki Loves Monuments/DEI research 2022/Final report/Introduction and have to be approved by a translation administrator.


Bayani Gabatarwa Abin koyo Shawarwari Matsalolin da za'a iya fuskanta Me ke cikin batutuwan? Ƙarin bayanai



Wurin bauta na Khandoba, Pune, Indiya: Mai-nasara WLM ta duniya, 2017

Duniyar da ke kewaye da mu tana sauyuwa a koda yaushe kuma tana ƙara habaƙa, haka ma hanyoyin da muke bi dan fuskantarta. Wannan kuma yana fassara ne zuwa hanyoyin da muka fahimci bambantuwa, daidaituwa da haɗuwa (Diversity, Equity and Inclusivity (DEI)). Asanda muke aiki game da zamar da Wiki Loves Monuments (Wiki na Ƙaunar Monuments) ta kasance mafi haɗuwa da daidaituwa, yana da mahimmanci mu bada hankalin mu ga gaskiyar cewa ra'ayinmu na 'haɗuwa da daidaituwa' na tasirantuwa ne akoda yaushe ga irin ƙwarewar da muka fuskanta a karan kanmu. Tsarin da ake bi dan cimma Bambantuwa, Daidaituwa da Haɗuwa dake buƙatar sake fuskanto abubuwan da muke zato da kuma ainihin ababen dake akwai.

A ƴan watannin da suka gabata na gudanar da binciken DEI, ta fitar mana da buƙatar dubiya akan wannan, kuma haƙiƙanin sanin cewa ba zai zama kawai irin mafita ce ta 'zubi daya ya dace da duka ba' matsalolin DEI bane. Tasgaron siyasa, al'adu da tattalin arziki sun nuna irin ababe sosai dake shiga da fice wurin kawo cikas da shafar aiwatarwa da samun nasarar waɗannan maslahohi.

Kowace tawagar shiryawa ta ƙasa na iya kasancewa a wani mataki daban na cimma DEI a ƙasarsu. Yayin da wasu na iya buƙatar magance matsalar samunkaiwa ga albarkatu da fasahun da za'a iya amfani da su don ƙara haɓaka mahalarta, wasu na iya buƙatar ƙarin tallafin kayan aiki don magance rashin shirye-shirye ga ƙananan hukumomi game da kulawar kayan tarihi.

A cikin kowane ɗayan waɗannan yanayin dole ne ka fara buɗe kullin farko don samun damar kaiwa gaba. Don haka, yana da kyau kawai a kalli DEI a matsayin gudanarwa wanda zai iya bayyana da ɗabbakuwa dan buƙatuttukan lokaci da sarari.

Wannan rahoton an fitar da shi ne daga zantuttukan da aka zayyana na cikin rahoton wucin gadi kuma ana fata ya bada babban fuska ga buƙatun Bambantuwa, Daidaituwa da Haɗuwar sanyowar kowa da samar da mafita ga fafutukar Wiki Loves Monuments.


Baya | Ƙarin karatu