Commons:Wiki Loves Monuments/Binciken DEI 2022/Rahoton ƙarshe/Abin Koyo

This page is a translated version of a page Commons:Wiki Loves Monuments/DEI research 2022/Final report/Learnings and the translation is 94% complete. Changes to the translation template, respectively the source language can be submitted through Commons:Wiki Loves Monuments/DEI research 2022/Final report/Learnings and have to be approved by a translation administrator.
Outdated translations are marked like this.


Bayani Gabatarwa Abin koyo Shawarwari Matsalolin da za'a iya fuskanta Me ke cikin batutuwan? Ƙarin bayanai



Haɗuwar kowa da Sanayyar al’umma

 

Wiki Loves Monuments gasa ce da aka haifo daga arewacin duniya. An ƙirƙiri tushen tsarinta ne bisa la'akari da buƙatun al'adu, tattalin arziki da siyasa na ƙasashen da suka ci gaba. Duk da yake an yi ƙoƙari na yau da kullun don sauya wannan son rai da kuma kasancewa cikin gogayya daga kudancin duniya, har yanzu akwai sauran fage da yawa da za'a rufe.

Kamar yadda rahoton wucin gadi ya bayyana, ƙasashe da dama na kokawa da yadda turawan mulkin mallaka suke kallon ababen kayayyakin tarihi na hukuma da kuma ƙin sanya al'ummomin da ba su da wakilci daga cikin su. Masu shiryawa na ƙasa daga ƙasa daban-daban, duk da haka, sun yi ƙoƙari su yi aiki a kan wannan batu ta hanyar yin amfani da jerin sunayen da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka tsara a cikin sassan kayan tarihi da kuma jawo hankalin jama'ar gari don matsa lamba ga ƙananan hukumomi su ƙara abubuwan tunawa da su a cikin jerin sunayen.

Muna rokon duk jama'ar gari da su tuntuɓi ƙananan hukumomi don ƙara abubuwan tarihin su a cikin jerin. - Brazil

Duk da wannan ƙoƙarce-ƙoƙarce, har yanzu akwai rashin gamsuwa a tsakanin wasu masu shirya gasar ta ƙasa game da ma'anar abin tunawa na yanzu da WLM ke amfani da shi. Suna jin cewa iyakance ma'anar abubuwan tunawa ga 'ginan nen abin tarihi' yana nufin nuna fahimtar yan mulkin mallaka ne ga abubuwan tarihi waɗanda bai ba da damar kayan tarihin yan kasa na asali ba. Wannan kuma yana rage kwarin gwiwa tsakanin al'ummomin yankin don shiga gasar daukar hoto da kuma kawo cikas ga hada kai.

Duk da haka, ba daidai ba ne a ɗauka cewa batun jerenta abubuwan tarihi na hukuma ba tare da haɗawa ba ya dace ne kawai ga kudancin duniya. Jerin abubuwan tarihi na ƙasa a yawancin ƙasashen yamma suna da hanya iri ɗaya na keɓancewa da kuma rashin yadda al'ummomin da aka ware. Akwai shirye-shiryen yiwuwar shawo kan hakan da wasu masu shirya taron na ƙasa suka yi. Koyaya dai, an gabatar da su tare da sabbin wahalhalu yayin aiwatar da waɗannan shirye-shiryen.

 
 

Taken ɗaukar hoto na tsorata wurare, an bijiro da shi ne dan magance sanyo mutanen Saami da jerin wuraren (tarihi)... Koyaya, al’ummomin basu sami jin daɗin ganin an ɗauki hoton wasu wuraren tarihin su ba - Finland

Ƙwarewa irin waɗannan da ke sama suna buƙatar dubawa cikin hanyoyin mu ga sanya haɗuwa, musamman a yanayin wuraren al'adu na asali. Wannan zai haɗa da magance tambayar yadda za mu ci gaba da mutunta damuwarsu game da keɓanciya da daidaitawa yayin tattara bayanai da yaɗa iliminsu. Wannan yana da mahimmanci musamman yayin da gasar WLM ta alaƙanci jama'a kuma buɗaɗɗen tushen bayanai ce, wanda zai iya sa wurarensu masu tsarki su zama masu sauƙi da 'kutsawa' ga masu ɗaukar hoto dake sha'awa. Don haka, gudanar da buɗaɗɗiyar tattaunawa tsakanin Wikimedians da al'ummomin ƴan asalin yankin game da ra'ayoyinsu da haɗa kai dan yaɗa ilimi na iya zama hanya ɗaya mai inganci ta nemo hanyar da ta dace game da wannan batu.

A taƙaice, yin tunanin haɗuwar sanya kowa shi ne tunani daga tabaran ganin irin waɗanda ba'a haɗu da su ba ko waɗanda aka keɓe. Ya kamata a samar da dabarun tsara su da yin la’akari da abin da al’umma ke bukata, maimakon abin da muke tunanin za su buƙata.

Sauya mahangar masu ɗaukar hoton

 

Ɗaya daga cikin manyan manufofin Wiki Loves Monuments shine tattara abubuwan tarihi masu alaƙa da al'adu a duk faɗin duniya ta hanyar hotuna. Koyaya, tun da gasar ɗaukar hoto ce, mahalarta da alƙalai sun ba da fifikon ƙyawun kayan tarihin da ingancin hotunan.

Yawancin gine-ginen (gina) ba a kiyaye su sosai… ba su da kyau sosai kamar kayan tarihin gado… Don haka mutane suke ƙoƙarin kin su ɗauki hotonsu. - Venezuela

Babu abin ƙarfafawa sosai don rubuta wasu gine-ginen tarihi (baccin shahararrun wuraren yawon buɗe ido). - Croatia

Mahalarta gaba ɗaya suna yin ƙwazo don ɗaukar hotuna masu kyau na 'kyawawan abubuwan tarihi, ma'ana waɗanda gwamnati ke kula da su sosai kuma sanannun wuraren yawon buɗe ido. Hakan ya faru ne saboda imanin da mahalarta ke yi ne na cewa ɗaukar irin waɗannan abubuwan tarihi zai basu hoto mai kyau da ka iya ba su damar samun nasara a gasar. Wannan yana haifar da rashin samun tara bayanan abubuwan tarihi na al'ummomin da ba'a sani ba saboda ba su da kariya kuma suna iya lalacewa saboda rashin matakan gwamnati.

Mun gabatar da nau'ukan kyaututtuka na musamman don ƙarfafa mahalarta su dauki hoto, kamar 'mafi kyawun hoto a kowane yanki', 'mafi kyawun hoto na tarihin Yahudawa', da sauransu. - Ukraine

Rubuta waɗannan abubuwan tarihi ba kawai yana haɓaka wakilci a gasar ba, har ma yana ba da sarari don fara tattaunawa, tsakanin al'ummomin gida da jami’oin tarihi na gargajiya, akan mahimmancin kiyaye waɗannan wurare. Misali, masu shirya WLM a Ukraine sun yada yadda gabatar da nau'ikan hotuna na musamman ba wai kawai ya taimaka musu wajen rubuta abubuwan tunawa da ke cikin haɗarin lalacewa, har ma sun taimaka wajen wayar da kan jama'a don taimakawa abubuwan tunawa da aka yi watsi da su a baya da aka jera a jerin abubuwan tarihi na hukuma.

Bugu da ƙari, ƙarfafa mahalarta su ɗauki hotunan abubuwan tunawa lokacin da ake amfani da su ta hanyoyi daban-daban, kamar a lokacin bukukuwa da sauran ayyukan al'umma ko yayin da aka dawo da su ta hanyar aikin rushewa ko sake dawowa, zai iya taimakawa wajen kawo ƙarin kayan aiki zuwa gare shi. labari irin waɗannan hotuna suna taimakawa ɗaukar ainihin wurin gadon da kuma rikitacciyar dangantakar da mutane ke tarayya da ita.

Abubuwan da suka shafi Jinsi

 

Abubuwan yau da gobe da suka shafi jinsi suna taka muhimmiyar rawa wajen tsara fahimtar mu da hangen nesan mu a duniya game da makewayenmu. Wannan yana bayyana ne musamman ta hanyoyin da muke hulɗa da al'adu da wuraren tarihi.

Misali, abubuwan tarihi da ke wajen birni gaba ɗaya ba a ɗaukar hotunan su saboda tsadar abin hawa ko kuma saboda damuwar tsaro. Wannan na ƙarshe ya zama abin hanawa musamman ga mata masu ɗaukar hoto, waɗanda za su iya gwammacewa ko dai su ziyarci abin tunawa a matsayin kungiya ko kuma da rana. A ɗaya bangaren kuma, mata na iya zama ba su samu damar zuwa wasu wurare a cikin wani abin tunawa ba, kamar wurin addini na aiki, saboda bambancin jinsi da ke nuni da ɓangarorin abin tunawa da za su iya ɗaukar hoto. Ta wannan hanyar jinsi yana ƙara samun girma ba kawai ga takardu ba, har ma ga ɗaukar hoton. Don haka, abubuwan tarihin da mai ɗaukar hoto ya ƙare da ɗaukar hotonsa, takamaiman abubuwan da aka ɗauka na rukunin da lokacin da aka ɗauki hoton duk suna magana game da gogewar jinsi. Waɗannan rikitattu ne a yadda mutane ke ɗanɗanawa da kuma yin alaƙa a sarari suna ƙara wa juna ilimi a dandalin Wikipedia.

Koyaya, wannan yanayin na iya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa. Iri ɗaya ko makamantansu na daƙile halarcin jinsi ba zai yi tasiri ba a kowace ƙasa da zata halarta. Haka aka ce, masu shirya gasar WLM suna bukatar sanin gaskiyar cewa shingayen dakatar jinsi na iya gabatuwa ta fuskoki daban-daban kuma yana da mahimmanci a lura da waɗannan shingayen don samun daidaito a gasar. Don haka, yana da mahimmanci a yi aiki don tabbatar da samun wakilcin jinsi a cikin matakai daban-daban na gasar.

Sanyo mata da dama wajen shirya WLM yana samar da yarda da kuma ƙara ƙarfafa mata a ƙasa. - Uganda

Bari mu fara, yana da mahimmanci yin la'akari da bambancin jinsi yayin kafa tawagar shirya gasar. Kamar yadda aka nuna a cikin abin da aka ambata a sama, samun mutane daga jinsi ɗaya kamar ku a cikin tawagar masu shiryawa na iya sa ku ji cewa ana ganin ku kuma ya ba ku fatan cewa za a yi la'akari da ra'ayoyin ku da abubuwan da kuka samu

A matsayina na mace a cikin harkar nan, a gare ni irin wannan yabo (fahimta a mahangar mace a cikin ayyukanmu) ya fi ƙarfi idan sun zo daga abokan aiki na maza. Yana sa ni jin goyon baya, kuma yana sa ni jin ina da abokan haɗin gwiwa waɗanda ke nuna wannan mahimmanci da dubiya fiye da hange kawai akan irin tasu jinsi. - Ciell, WLM-na duniya

Koyaya, samun mutane daga jinsi daban-daban a cikin tawagar kaɗai ba zai taimaka ba. Domin samun daidaito a gasar muna kuma buƙatar mu tuna cewa wasu jinsin na iya, idan aka yi la’akari da asalinsu, su kasancewa na baya wajen samun albarkatu da ake buƙata don shiga gasar. Misali, masu shirya gasar daga Brazil da Uganda sun bayyana yadda, idan aka kwatanta da maza, mata a ƙasar suna fuskantar wahalar samun albarkatu kamar na’urorin ɗaukar hoto da intanet waɗanda su ne ainihin buƙatuwa don samun damar shiga gasar ɗaukar hoto na dijital kamar WLM. Wannan yana buƙatar ƙarin yunƙurin mayar da hankali don kulle giɓin shiga a tsakanin jinsi da kuma sa WLM ta zama mai daidaituwa. Waɗannan na iya kasancewa ta hanyar tsara yawon ɗaukar hoto, tanadin albarkatu, kasafi da tallafin yin tafiye-tafiye da sauransu.

Tare da faɗin haka ne, yana da mahimmanci a jaddada buƙatar dubiya fiye da na nau’in jinsi biyu yayin aiki don sanya haɗowar jinsi. Al'ummar LGBTQI+ galibi ba su da wakilci kuma an ware su a rubuce-rubucen tarihi kuma galibi ana ganin tarihinsu ba su da mahimmanci. Samun jama’a daga al’umman wajen shirya gasar a wuraren su tare da hada abubuwan tarihinsu a gasar ƙasa da ƙasa, zai taimaka mana wajen samar da yanayin alaƙar cuɗanya da haɗa kai ga kowa.

Harshe da Sadarwa

Harshe yana taka muhimmiyar rawa wajen sadar da basirori, buƙatu da yaɗa ilimi. Rashin samun damar kaiwa ga ilimi a cikin yaren ku na iya kawo cikas ga ƙoƙarin fahimtar aikin da ke hannunku kuma yana iyakance shigar ku cikin gangamin baki ɗaya. A wani batun, yana iyakance haduwar mahalarta mabanbanta daga ƙasashe waɗanda ba ƴan asalin jin turanci ba ne.

Akwai sadarwa a (WLM-i) amma matsalar ita ce shingen dake harshe… wani lokacin yana da wuya a fassara rubutun zuwa Espanya - Venezuela

Waɗannan giɓayen amfani da harshe za'a iya magance su cikin sauƙi ta hanyar ƙara adadin fassarar bayanai na tallata shirin da albarkatu cikin harsunan gida. Duk da haka, abu ɗaya mai mahimmanci da ya kamata mu sa a rai wurin aiki da fassarar shi ne cewa wasu lokuta kalmomi suna ɗaukar wata ma'ana daban a cikin wani harshe da al'adu daban.

Masu halartar an ruɗa su da kalmar “monuments” (ababen tunawa na tarihi) waɗanda suka shafi gine-gine a wuraren jama'a. - Philippines

Al’ummomi na gida da masu shiryawa na iya alaƙa da kuma gano wata kalma daban ƙarƙashin jigon da aka sanya. Yana taimakawa wajen sanya waɗannan rikitarwa na harshe a zuciya yayin tsara dabarun sadarwa a cikin yankunan harshen.

Notes

1.^ Irin wasu matsaloli na rashin kaiwa zai iya zaba ba kawai na jinsi ba ne. Ajujuwa, matsayar mutum a al'umma, fanni, nakasar, da sauran su., Na iya shiga cikin waɗannan.
2.^ Tawagar WLM sun samu grant da su shirya fassara na zaɓaɓɓun daftarai ɗin gasar WLM zuwa harsunan duniya 12 kuma muna sa ran yayi aiki wurin rage shange na harshe.


← Baya | Ƙarin karatu →